Hukumar Hisbah a jihar Sokoto ta sanar da cewa tana neman matasan ‘yan Tiktok biyu ruwa a jallo a faɗin jihar.
Mutanen da ta ke nema sun hada da Y. America da Asma’u Gorgeous.
A cewar sanarwa daga mukaddashin kwamanda, Imam Sirajo Abubakar, jami’an hukumar sun bazu zuwa wurare daban-daban a ranar Talata domin gano su tare da kamasu.
Hukumar ta ce wannan aiki na ci gaba ne a matsayin wani ɓangare na aikinta na tabbatar da doka da oda a Sokoto State.