Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da rasuwar fitaccen mawaƙin siyasa, Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka, wanda ya rasu ranar Lahadi yana da shekara 47 a duniya.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Lahadi.
Bisa bayanan da iyalansa suka bayar, Kosan Waka ya rasu ne ranar Lahadi, kuma za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar a ƙauyen Tsanni da ke ƙaramar hukumar Batagarawa a Jihar Katsina.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, musamman mahaifiyarsa, da abokansa, masu mu’amala da shi, masoyansa da kuma al’ummar Jihar Kano baki ɗaya.
A cewar gwamnan, marigayi Kosan Waka ɗan asalin Jihar Katsina ne mai kishin ƙasa wanda ya zauna a Kano, kuma waƙoƙinsa sun zarce siyasa wajen haɗa kan jama’a, bunƙasa al’adu da wayar da kan al’umma.
Gwamnan ya ce:
“Waƙoƙinsa sun zarce siyasa, sun kasance wata muhimmiyar hanya ta inganta haɗin kai, al’adu da wayar da kan jama’a.”
Ya kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata kabarinsa, Ya shigar da shi Aljannatul Firdausi, tare da bai wa iyalansa juriyar wannan babban rashi.
Sanarwar ta bayyana cewa Kosan Waka na daga cikin fitattun mawaƙan siyasa na Kano, inda hazakarsa, ƙirƙira da salon waƙoƙinsa suka sa ya samu karɓuwa a sassa daban-daban na Najeriya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya haɗa kai da masana’antar nishaɗi da miliyoyin masoyan marigayin a faɗin Najeriya wajen alhinin wannan rashi, tare da addu’ar Allah Ya yi masa rahama.