Gidauniyar Digital Justice and Sustainable Development ta shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, kan zargin cewa manhajar TikTok ta takaita amfani da dandalinta ga wasu masu amfani da ke jihohin Arewacin Najeriya.
A cikin ƙarar da Daily Trust ta gani, ƙungiyar ta yi zargin cewa TikTok ta sanya takunkumi ko kuma ta toshe masu amfani da manhajar da ke Kaduna, Kebbi, Kano da Sokoto daga shiga dandalin.
Ƙungiyar, ta hannun lauyanta, Festus Ogun, ta roƙi kotun da ta tantance ko takunkumin da ake zargin TikTok ta sanya ya saɓa wa haƙƙin ’yan ƙasa na faɗin albarkacin baki da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada, sannan ko hakan ya zama nuna wariya ga masu amfani da manhajar a jihohin da abin ya shafa.
An shigar da ƙarar ne a ranar 5 ga Oktoba, 2026, bisa tanadin sashe na 39, 42, 45 da 46 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da Dokokin Kare Haƙƙoƙin ’Yan Adam na Asali na 2009, da kuma tanade-tanaden Yarjejeniyar Afirka kan Haƙƙoƙin ’Yan Adam da na Al’umma.
Mai ƙarar ta ce TikTok ba za ta iya takaita amfani da dandalinta ga masu amfani da ke jihohin Arewa da abin ya shafa ba, yayin da take barin masu amfani da ke wasu sassan ƙasar su ci gaba da amfani da manhajar ba tare da takura ba.
Ta buƙaci kotun ta ayyana takunkumin da ake zargin TikTok ta sanya a matsayin “ba daidai ba ne, ya saɓa wa kundin tsarin mulki kuma an yi shi ba tare da ka’ida ba”, tana mai cewa hakan ya take haƙƙin masu amfani da manhajar na faɗin albarkacin baki da kuma samun kariya daga nuna wariya.
Ƙungiyar ta kuma nemi kotun ta bayar da umarnin cewa TikTok ta gaggauta cire takunkumin da ake zargin ta sanya, tare da hana kamfanin sake takaita amfani da manhajar ga mutanen Arewacin Najeriya ko wani ɓangare na ƙasar ba tare da sahihin dalili na doka ba.
Haka kuma, ta roƙi kotun da ta umarci TikTok ta wallafa takardar neman afuwa ga jama’a a jaridun ƙasa guda uku, bisa zargin take haƙƙoƙin ƙungiyar na asali.
Mai ƙarar na son kotun ta tantance ko toshe masu amfani da TikTok a wasu jihohi ya saɓa wa sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulki, wanda ke ba da tabbacin ’yancin faɗin albarkacin baki, da kuma sashe na 9 na Yarjejeniyar Afirka.
Haka kuma, tana son kotun ta tantance ko bambancin yadda ake ba masu amfani da TikTok damar shiga dandalin a sassan Najeriya ya saɓa wa sashe na 42 na Kundin Tsarin Mulki da sashe na 2 na Yarjejeniyar Afirka, waɗanda suka haramta nuna wariya.
An shigar da ƙarar ne a Sashen Abuja na Babbar Kotun Tarayya, inda aka sanya TikTok Inc, mai adireshi a Culver City, California, a Amurka, a matsayin wanda ake ƙara.
Kotun ta umarci wanda ake ƙarar da ya gabatar da sanarwar bayyana kansa a cikin kwanaki biyar daga ranar da aka kai masa sammaci, idan ba haka ba kotun za ta iya bayar da umarnin da ta ga ya dace bisa doka.