Wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin yara sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta gaggauta kaddamarwa da fara aiki da Kwamitin Kare Yara na jihar domin inganta kariya ga yara marasa galihu.
A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa, Cibiyar Legal Orientation and Humanitarian Aid Initiative (CELOHA Nigeria) da West Africa Network for Child Protection (WAN Network) sun bayyana damuwa kan ci gaba da jinkirin fara aiki da kwamitin, duk da kokarin gwamnati wajen samar da manufofin kare yara.
Ƙungiyoyin sun ce yara da dama a Kano na fuskantar matsaloli masu tsanani kamar cin zarafi, sakaci, amfani da su wajen aiki, safarar yara, bara a titi, auren wuri da kuma tashin hankali. Sun ce waɗannan matsaloli na bukatar gaggawar mataki da haɗin gwiwa daga hukumomin da abin ya shafa.
A cewarsu, ya kamata a mayar da hankali wajen ƙarfafa tsarin kare yara, tallafa wa iyalai masu rauni, inganta hanyoyin tura rahoto da kuma tabbatar da haɗin gwiwar hukumomi da ke da alhakin kare haƙƙin yara.
Sun bayyana cewa Kwamitin Kare Yara zai haɗa ma’aikatu na gwamnati, hukumomin tsaro, ƙungiyoyin farar hula, shugabannin al’umma da abokan hulɗa na ci gaba domin daidaita ayyukan kare haƙƙin yara.
Ƙungiyoyin sun yi gargaɗi cewa duk ranar da aka ƙara jinkiri, yara masu rauni na ƙara shiga cikin haɗari.
Sun roƙi gwamnatin Kano da ta gaggauta fara aiki da kwamitin, ta ware isassun kuɗaɗe don ayyukan kare yara, ta ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙungiyoyin farar hula, tare da tabbatar da aiwatar da dokoki da manufofin kare yara.
Haka kuma sun bukaci a riƙa sa ido akai-akai da tabbatar da lissafi kan duk wani cin zarafin yara.
CELOHA Nigeria da WAN Network sun ce za su ci gaba da aiki tare da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin gina tsarin kare yara mai ƙarfi da zai kare haƙƙi da rayuwar kowane yaro a jihar Kano.