Saturday, October 17, 2026
HomeLafiyaAn dakatar da likita a FMC Daura kan jinkirin kula da mara...

An dakatar da likita a FMC Daura kan jinkirin kula da mara lafiya

Asibiti na ci gaba da bincike yayin da iyalan marigayiyar suka bai wa asibiti wa’adin kwanaki 14

Hukumar gudanarwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC), Daura, ta dakatar da wani likita na tsawon watanni uku saboda zargin jinkirin ba da kulawa ga wata mara lafiya da ta rasu bayan an tura ta wani asibiti.

Daraktan lafiya na asibitin, Dakta Umar Farouk, ya tabbatar da hakan yayin da yake mayar da martani kan korafin da iyalan marigayiyar suka gabatar ta hannun lauyoyinsu.

Ya ce an kawo marigayiyar FMC Daura ne daga Asibitin Sojoji na Daura a ranar 23 ga Afrilu bayan ta samu matsala sakamakon karin jini da aka yi mata a asibitin da ta fito.

Ya bayyana cewa an fara kwantar da ita a sashen gaggawa (A&E) kafin daga baya a tura ta sashen kulawa ta musamman (ICU).

Dakta Farouk ya amince cewa likitan da ke bakin aiki a lokacin ya yi jinkirin zuwa, lamarin da ya sa dole ya shiga cikin lamarin da kansa.

“Marar lafiyar ta zo cikin mummunan hali, kuma da aka fahimci cewa likitan da ke bakin aiki bai amsa kira cikin lokaci ba, aka kira ni da sassafe,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Na isa asibiti wajen karfe 4 na safe, na duba ta, na yi mata farfaɗowa, sannan na daidaita halinta a ICU.”

Ya ce asibiti nan take ya umarci sashen bincike na SERVICOM da ya gudanar da bincike kan abin da ya faru.

Bayan kammala binciken, aka mika rahoto ga hukumar gudanarwa wadda ta dauki matakin ladabtar da likitan.

“An mika rahoton bincike ga shugabancin asibitin, kuma an dakatar da likitan na tsawon watanni uku yayin da ake ci gaba da bincike,” in ji Dakta Farouk.

Ya ce daga baya dangin marigayiyar sun bukaci a tura ta zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, kuma an amince da hakan, tare da samar da motar daukar marasa lafiya da ma’aikaciyar ICU domin rakiyar ta.

Ya ce daga baya ne suka samu labarin cewa ta rasu a Katsina, amma ba su da cikakken bayani kan abin da ya faru a can.

Dakta Farouk ya kuma ce ya jagoranci tawagar jami’an asibiti domin yin ta’aziyya ga iyalan mamaciyar.

A halin yanzu, wani kamfanin lauya da ke Kano, Abdullahi Mohammed & Co. (Jurist Chamber), mai wakiltar iyalan marigayiyar, ya bai wa asibitin wa’adin kwanaki 14 domin kammala bincike da kuma sanar da matakan ladabtarwa da aka dauka.

Daraktan ya tabbatar da karɓar takardar lauyoyin, inda ya ce an tura batun zuwa sashen shari’a na asibitin.

Ya ce asibitin ya riga ya mayar da martani ta hannun jami’in shari’a, yana bayyana matakan da aka dauka, daga ciki har da dakatar da likita da kuma ci gaba da bincike, yana kuma roƙon iyalan su bari a bi ka’ida.

Dakta Farouk ya jaddada cewa asibitin na da cikakken niyyar tabbatar da gaskiya da adalci, yana mai cewa duk ma’aikacin da aka tabbatar da laifinsa bayan kammala bincike zai fuskanci hukunci mai dacewa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments