Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun daƙile wani yunƙurin satar mutane a hanyar Enugu–Otukpo, inda suka ceto mutum uku ba tare da wani rauni ba.
A cikin wata sanarwar da ta fitar a shafina na X, rundunar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 25 ga Fabrairun 2026, lokacin da sojoji ƙarkashin Operation WHIRL STROKE suke gudanar da sintirinsu na dare daga sansaninsu da ke Otukpo.
A yayin sintirin ne sojojin suka samu sahihan bayanai kan motar fasinjoji da ta saci mutanen inda sojojin suka tafi wurin nan take, suka bi sawun motar inda suka kama masu satar mutanen a hanyarsu ta tserewa.
Sanarwar ta ce ba a samu wata arrangama tsakanin sojojin da masu garkuwa da mutanen ba saboda sun tsere inda suka bar mutanen da suka sace.
Kakakin rundunar ya shawarci direbobi da su lura da rashin motsin motoci a tazara mai kimanin kilomita biyu da kuma dakata wa don tantance yanayi idan akwai abin da bai dace ba.