Hukumar kula da sauye-sauyen gwamnati kan samar da lantarki a Najeriya, NISO ta bayyana cewa matsalar ƙarancin wutar lantarki da ake fuskanta a ƙasar na da nasaba da ƙarancin isar gas zuwa tashoshin samar da wuta.
A cewar hukumar, matsakaicin ƙarfin samar da wuta a yanzu na kusan megawatt 4,300 ya dogara ne da ƙarancin gas da ake samu a tashoshin samarwa.
Hukumar ta ce tashoshin ne suke samar da mafi yawan wutar lantarki a ƙasar, don haka duk wani tangarda ko ƙaranci a isar gas yana tasiri kai tsaye kan ƙarfin samar da wuta da kuma yawan wutar da ke shiga kamfanin rarraba wutar.
Hukumar ta yi alƙawarin ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki don ganin an dawo da cikakken isar wuta da zarar isar gas ta inganta kuma ƙarfin samarwa ya dawo yadda ya kamata.
Duk da cewa wannan yanayi na iya haifar da matsala ga masu amfani da wuta, NISO ta yi kira ga jama’a da su fahimci halin da ake ciki a yanzu.