Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, da shugaban hukumar kare haƙƙin bil’adama, Volker Türk, sun yi tsokaci kan halin da ake ciki a rikicin da ya barke tsakanin Afghanistan da Pakistan.
Guterres ya yi kira ga ƙasashen biyu da su bi doka da ƙa’idojin kasa da kasa ba tare da tangarda ba, musamman ma dokokin jin ƙai na kasa da kasa.
A nasa bangaren, Türk ya yi kira ga Afghanistan da Pakistan da su shiga tattaunawa don shawo kan rikice-rikicen kan iyaka da harin jiragen saman da ke kashe mutane.