Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaJiga-jigan jam'iyya na shirin tarbar Gwamnan Kano Abba zuwaAPC

Jiga-jigan jam’iyya na shirin tarbar Gwamnan Kano Abba zuwaAPC

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

Kungiyar tsohon Minista ta ATM Gwarzo ta nuna goyon baya ga yiwuwar sauya sheƙar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

Kungiyar ta bayyana cewa sauya shekar Gwamnan za ta jawo kusanci tsakanin Kano da gwamnatin tarayya, kuma za a samu tagomashi

Ta tabbatar wa gwamnan cikakken goyon baya domin haɗin kai da cigaban jihar, inda ta fara yi masa maraba da shirin shiga APC

Kungiyar tsohon Minista Abdullahi Tijjani Gwarzo ta ATM Gwarzo ta bayyana farin cikinta kan rahotannin da ke cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na iya ficewa daga NNPP zuwa APC.

A cewar kungiyar, wannan mataki zai zo a kan lokaci mai kyau kuma zai amfani Kano ta fannoni da dama da jawo ci gaba mai dorewa.

Wannan dai na kunshe a cikin wata sanarwar, da Kabiru Salihu Bako, Babban Sakatare na Musamman ga Abdullahi Tijjani Gwarzo ya sanya wa hannu kuma aka wallafa ta a shafin Facebook na kungiyar.

Kungiyar ta ce idan Kano ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya, hakan zai buɗe ƙofofin haɗin gwiwa mai ƙarfi, da kuma hanzarta aiwatar da ayyukan raya ƙasa a jihar.

ATM Gwarzo ta jaddada cewa haɗin kai tsakanin jiha da tarayya na da matuƙar muhimmanci wajen cimma muradun jama’a da ci gabansu.

Bayan haka, ta ce manufofi da sauye-sauyen da ake aiwatarwa a matakin tarayya sun samar da ingantaccen tubali da Kano za ta iya amfani da shi domin bunƙasa tattalin arziƙi.

Haka kuma kungiyar na ganin hakan zai kara inganta shugabanci, da kuma bunƙasa ababen more rayuwa a sassa daban-daban na jihar Kano. A cewar sanarwar:

“Muna ganin wannan mataki ba kawai ya zo a kan lokaci ba ne, abu ne da ya dace, musamman idan aka yi la’akari da irin gagarumin ci gaban da ake samu a halin yanzu.” “Manufofi da tsare-tsaren da ake aiwatarwa sun samar da ingantaccen tsari na cigaba mai ɗorewa, farfaɗo da tattalin arziƙi, da gina manyan ababen more rayuwa, wanda hakan zai amfani Kano matuƙa.”

Kungiyar ta kara da cewa kusantar gwamnatin tarayya za ta taimaka wa Kano wajen samun kyakkyawan sauƙin aiwatar da ayyuka a bangaren lafiya da sauransu.

Ta bayyana cewa idan aka samu cikakken fahimta da haɗin kai, jama’ar Kano za su fi cin gajiyar shirye-shirye da tallafin da ke fitowa daga matakin tarayya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments