Saturday, October 17, 2026
HomeWasanniƘasashe 3 sun samu nasarar tsallakawa zagayen ƴan 16 na gasar AFCON

Ƙasashe 3 sun samu nasarar tsallakawa zagayen ƴan 16 na gasar AFCON

Zuwa yanzu ƙasashe 3 sun samu nasarar tsallakawa wasannin zagayen ƴan 16 na gasar cin kofin Afrika wato AFCON da ke ci gaba da gudana a Morocco, ƙasashen da suka ƙunshi Masar da Najeriya da kuma Algeria.

Masar ce ƙasa ta farko da ta samu nasarar tsallakawa zagayen ƴan 16 bayan doke Afrika ta kudu da ƙwallo 1 mai ban haushi a Juma’ar da ta gabata, yayin wasan da ya gudana a filin wasa na Adrar da ke Agadir.

The Pharaohs ta kammala wasan da ƴan wasa 10 bayan korar ɗan wasan bayan ta Mohammed Hany sakamakon katin gargaɗi har biyu wanda aka bi bayansa da katin kora wato jan kati.

A minti na 45 ne Mohammed Salah na Liverpool ya zurawa Masar ƙwallon ɗaya tilo wanda ke nuna Masar ta tsallaka matakin na gaba tare da kuma da wasa 1 a gabanta, bayan gagarumar nasararta kan Zimbabwe da ƙwallaye 2 da 1 wanda Salah da Marmoush suka zura.

Ƙasa ta biyu a wannan jeri ita ce Najeriya, wadda ta samu nasarar tsallakawa zagayen ƴan 16 bayan lallasa Tunisia da ƙwallaye 3 da 2 ƙwallayen da Super Eagles ta samu daga hannun ƴan wasanta Victor Osimhen da Wilfred Ndidi da kuma Ademola Lookman.

Idan ba a manta ba, dama tawagar ta Najeriya ta buɗe wasanta na farko da nasara kan Tanzania da ƙwallaye 2 da 1 wanda ya bata jagoranci a rukuninta na C.

Ta 3 kuma ta ƙarshe a iyakar ƙasashen da suka tsallaka zagayen na ƴan 16 kawo yanzu ita ce Algeria wadda yanzu haka ke da yawan maki 6 bayan doka wasanni 2 a wannan gasa inda ta ke jagorancin rukuninta na E.

Tawagar ta Desert Foxes ta doke Burkina Faso ne da ƙwallo 1 mai ban haushi a jiya Lahadi wanda ya bata damar shiga wannan jeri, ƙwallon da ta samu ta hannun tauraronta Riyad Mahrez.

Algeria wadda ta taɓa lashe kofin wannan gasa a shekarar 1990 da kuma 2019 tana gaban ƙasashen Burkina Faso da Sudan waɗanda ke rukuni ɗaya da ita.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments