Rundunar ƴan sanda a Zamfara ta ce ta daƙile wani yunkurin ƴan bindiga na kai hari a karamar hukumar Maru na jihar a safiyar yau Lahadi.
A cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce sun samu nasarar daƙile yunkurin ne bayan samun bayanan sirri.
“Haɗakar jami’an tsaro ne da ya haɗa ƴansanda, sojoji, rundunar tsaro ta al’umma da kuma ƴan sa-kai suka fafata da maharan, abin da ya tilasta musu tserewa tare da raunuka.
Babu wanda ya mutu ko kuma garkuwa da aka yi,” in ji sanarwar ƴan sandan.
Sai dai, an tsaurara matakan tsaro a karamar hukumar ta Maru da kuma yankuna da ke ƙewaye.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba ya tabbatarwa al’umma cewa a shirye jami’an tsaro suke wajen kare rayuka da kuma dukiyoyinsu, inda ya buƙace su da su ci gaba da bai wa hukumomi haɗin kai.