Monday, November 9, 2026
HomeLabaraiLabaraiSarkin Musulmi ya danganta bara da almajirai ke yi da talauci

Sarkin Musulmi ya danganta bara da almajirai ke yi da talauci

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce talauci ne ke tilasta wa yara da dama yin bara a tituna, duk da cewa yawancinsu na son zuwa makaranta.

Sarkin ya yi wannan bayani ne a taron shekara-shekara na kungiyar tsofaffin daliban Barewa (BOBA) na shekarar 2026, da aka gudanar a Gombe.

Ya ce yara da ke yawo a tituna suna neman abinci galibi talauci ne ya hana su samun ilimi, ba wai rashin sha’awar karatu ba.

Ya bayyana karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta a matsayin babbar matsala da ke barazana ga tsaron kasa da ci gabanta.

Sarkin ya jaddada muhimmancin ilimin addini da na zamani, yana mai cewa Musulunci bai amince da bara ba, kuma ya kamata al’umma su hada kai wajen magance matsalar.

Ya kuma bukaci gwamnatoci su samar da damar ilimi da koyon sana’o’i ga yara marasa galihu.

A karshe, ya yaba wa gwamnatocin Gombe da Zamfara kan shirye-shiryen da suka samar domin almajirai su hada karatun Alkur’ani da na zamani, tare da kira ga sauran jihohi su yi koyi da su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments