Saturday, November 14, 2026
HomeLabaraiLabaraiAPC ta bukaci a hukunta waɗanda suka tarwatsa taron Peter Obi a...

APC ta bukaci a hukunta waɗanda suka tarwatsa taron Peter Obi a Legas

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi kira ga jami’an tsaro da su gudanar da bincike tare da hukunta waɗanda suka kai hari kan taron magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, a jihar Legas ranar Alhamis.

A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, APC ta yi Allah-wadai da harin, tare da buƙatar hukumomin tsaro su tabbatar an hukunta waɗanda suka aikata hakan.

Haka kuma, jam’iyyar ta jaddada buƙatar tabbatar da zaman lafiya da tsaro yayin harkokin siyasa, inda ta yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani abu da ka iya haddasa rikici a ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments