Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta ce ba za ta ɗauki mataki kan rikicin shugabancin jam’iyyar ADC ba, har sai ta samu cikakken kwafin hukuncin kotun da ta soke shugabancin David Mark.
Kwamishinan hukumar na ƙasa, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Sunday PUNCH, inda ya ce INEC za ta fara nazarin hukuncin kafin yanke shawarar matakin da ya dace ta ɗauka.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta tattauna batun a taronta na mako mai zuwa, tare da tabbatar da bin duk wani umarnin kotu idan aka ɗaukaka ƙara kuma aka samu umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin.
Wannan na zuwa ne bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin soke shugabancin David Mark da wasu matakan da kwamitinsa ya ɗauka, ciki har da zaɓen fidda gwani da ya samar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Nafiu Bala Gombe ya shigar, inda ya ƙalubalanci tsarin da aka bi wajen naɗa shugabannin jam’iyyar.