Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar (ADC-PCC) ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, duk da abin da ta bayyana a matsayin tsoratarwa, tashin hankali da kuma amfani da hukumomin gwamnati wajen matsa wa ’yan adawa lamba.
Ƙungiyar ta kuma zargi gwamnatin jam’iyyar APC da yin amfani da hukumomin tsaro da kuma yin maguɗi a tsarin shari’a domin ci gaba da riƙe madafun iko.
Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ADC-PCC, Kola Ologbondiyan, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar an Abuja.
Ologbondiyan ya ce hare-haren da ake zargin ana kai wa mambobin jam’iyyun adawa da magoya bayansu a sassan ƙasar na barazana ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Ya ambaci kisan wasu mambobin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a Jihar Delta, inda ya yi zargin cewa lamarin ya biyo bayan hari da wasu da ake zargin ’yan daba ne masu goyon bayan APC suka kai wa wurin gangamin jam’iyyar.
Ya kuma ce ana samun irin waɗannan hare-hare kan mambobin ADC, NDC da Allied Peoples Movement (APM) a jihohin Kaduna, Kogi, Katsina, Kebbi da Sokoto.
Ya bayyana lamarin a matsayin barazana ga ’yancin dimokuraɗiyya.
Haka kuma, ADC-PCC ta nuna damuwa kan shirin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da kuma ikirarin cewa an yi kutse cikin bayanan rajistar masu zaɓe, tare da zargin cewa an naɗa wasu masu goyon bayan APC a muhimman muƙamai a hukumar.
Ƙungiyar ta kuma zargi jami’an tsaro da amfani da ikonsu wajen tsoratarwa, kamawa da muzgunawa ’yan adawa.
Ologbondiyan ya yi zargin cewa wani darakta mai ci a wata hukumar tsaro na cikin majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta APC a matsayin mataimakin darakta mai kula da harkokin tsaro da leƙen asiri. Ya ce hakan ya saɓa wa dokar da ta kafa hukumar.
A cewar sanarwar, ADC-PCC ta ce ba za a iya tabbatar da sake zaɓen Tinubu ta hanyar amfani da tsarin shari’a ko hukumomin zaɓe da ake zargin an yi wa maguɗi ba. Ƙungiyar ta kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su kasance cikin shiri wajen kare ƙuri’unsu, haƙƙoƙinsu na dimokuraɗiyya da ’yancinsu na kundin tsarin mulki.
Bugu da ƙari, ta buƙaci ƙasashen duniya, ƙungiyoyin farar hula, shugabannin addinai da na gargajiya da su sanya ido kan yanayin siyasa da tsaro a Nijeriya gabanin zaɓen 2027. Ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su kasance masu nuna adalci ga dukkan jam’iyyun siyasa.
Sanarwar ta ƙare da cewa zaɓen 2027 dole ne ya nuna ainihin ra’ayin ’yan Nijeriya, tare da jaddada cewa babu wata barazana ko tashin hankali da zai hana al’umma yanke shawarar wanda suke so ya jagorance su.