Dakarun rundunar Operation Enduring Peace (OPEP) sun kama wasu mutum uku da ake zargi da hannu a kisan wasu ma’aurata bisa zargin maita a Jihar Plateau.
Waɗanda aka kashe su ne Abdullah Adamu, mai shekaru 58, da matarsa, Habiba Ibrahim, mai shekaru 45, a kauyen Tabga/Dogon Ruwa da ke yankin Bashar, a Ƙaramar Hukumar Wase ta jihar.
Rahoton Zagazola Makama ya ce dakarun rundunar Sector 2 ta OPEP sun kama waɗanda ake zargin ne ranar Laraba, bayan samun rahoton kisan ma’auratan.
Biyu daga cikin waɗanda aka kama sun haɗa da Hussaini Mallam Yusufu, mai shekaru 22, da Ishaku Sule, mai shekaru 24, yayin da ba a bayyana sunan mutum na uku ba.
Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun shaida wa jami’an tsaro cewa sun yi mafarki ne, inda suka ga matar, Habiba Ibrahim, a matsayin mayya.
Rahoton ya ƙara da cewa ana ci gaba da tsare waɗanda ake zargin domin gudanar da cikakken bincike da kuma ɗaukar matakin da ya dace.