Saturday, November 7, 2026
HomeLabarai’Yan sanda sun tsare jami’insu kan harbin da ya kashe yarinya ’yar...

’Yan sanda sun tsare jami’insu kan harbin da ya kashe yarinya ’yar shekara biyu a Legas

Rundunar ’yan sandan Legas ta tsare wani jami’inta mai mukamin ASP, Omotayo Olajide, bayan harbin bindiga ya kashe yarinya ’yar shekara biyu a Ajegunle.

Rundunar ’yan sandan Legas ta tsare wani jami’inta mai mukamin ASP, Omotayo Olajide, bayan harbin bindiga ya kashe yarinya ’yar shekara biyu a Ajegunle.

Lamarin ya faru ne a daren Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026, inda wata yarinya kuma ta jikkata. Mamaciyar mai suna Omole Taiwo ta rasu bayan kai ta asibiti.

Kakakin rundunar, SP Abimbola Adebisi, ta ce an tura jami’an yankin ne bayan rikicin ƙungiyoyin Nosamu Boys da Alayabiagba Boys kan karɓar kuɗin haraji.

Ta ce a yayin aikin, ASP Olajide ya harba bindiga, harsashin ya samu yaran biyu. An garzaya da su asibiti, amma Omole ta rasu daga bisani a LASUTH.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Tijani Fatai, ya ce an kwace bindigar jami’in tare da tsare shi, yayin da aka miƙa binciken ga sashen SCID. Ya tabbatar wa iyalan mamaciyar cewa za a yi adalci, kuma ba za a kare duk wanda aka samu da laifi ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments