Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiZa a kammala kafa ’yan sandan jihohi kafin Disamba 2026 — Bamidele

Za a kammala kafa ’yan sandan jihohi kafin Disamba 2026 — Bamidele

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce ana sa ran kammala matakan kafa ’yan sandan jihohi a Najeriya kafin ko zuwa Disamba 2026.

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce ana sa ran kammala matakan kafa ’yan sandan jihohi a Najeriya kafin ko zuwa Disamba 2026.

Ya bayyana cewa majalisun dokokin jihohi akalla 30 sun amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai ba da damar kafa rundunonin ’yan sanda a jihohi.

Bamidele ya ce wannan amincewa ta cika sharadin kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi da kundin tsarin mulki ya tanada.

Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabi a Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru, Jihar Plateau.

A cewarsa, Majalisar Dokoki ta Ƙasa za ta tattara rahotannin jihohin, ta amince da kudirin, sannan ta miƙa shi ga Shugaban Ƙasa domin sa hannu.

Ya jaddada cewa kafa ’yan sandan jihohi ba wai samar da rundunonin sojojin siyasa ba ne, illa dai inganta tsaro a matakin al’umma tare da tanadin dokoki da za su kare haƙƙin bil’adama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments