Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba ta da wata matsala da ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Abdussalam Gwarzo, tana mai cewa umarnin kotu ne ya hana ta saka sunansa cikin jerin ’yan takarar zaɓen 2027 da ta sabunta.
Wani babban jami’in hukumar ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa INEC ta tantance tare da amincewa da takarar Gwarzo, amma ba za ta iya wallafa sunansa ba har sai an samu hukuncin ƙarshe kan umarnin kotu.
Jami’in ya bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ce ta bayar da umarnin wucin gadi (Ex Parte) a ranar 27 ga Oktoba, wanda ya shafi saka sunan ɗan takarar cikin jerin sunayen ’yan takara.
Hakan na nufin cewa cire sunan Gwarzo daga jerin da aka sabunta ba wai saboda INEC ta ƙi amincewa da takararsa ba ne, a cewar jami’in hukumar, sai dai saboda umarnin kotu da take bin sa.