Gwamnan jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar (APM), Seyi Makinde, ya soki manufofin gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Makinde ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kundin manufofinsa mai taken Reset Agenda a Abuja, gabanin zaɓen shugaban ƙasa da aka shirya gudanarwa ranar 16 ga Janairu, 2027.
A cewarsa, babbar matsalar Najeriya ba ƙarancin albarkatun ƙasa ba ce, illa ƙarancin sabbin dabaru da hangen nesa wajen shugabanci.
Ya ce Najeriya ƙasa ce mai tarin albarkatun ƙasa da kuma ƙwararrun mutane, amma abin takaici, shugabanninta ba sa amfani da basira da sabbin dabaru wajen tafiyar da al’amuran ƙasar.
Makinde ya jaddada cewa akwai buƙatar sauya salon shugabanci domin amfani da albarkatun ƙasar yadda ya kamata wajen inganta rayuwar ’yan Najeriya.