Friday, November 6, 2026
HomeLabarai’Yan bindiga sun sace malamar firamare a jihar Nasarawa, sun nemi Naira...

’Yan bindiga sun sace malamar firamare a jihar Nasarawa, sun nemi Naira miliyan 50

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wata malamar makarantar firamare, Amina Hussaini, a gidanta da ke ƙauyen Kuru, Ƙaramar Hukumar Toto ta Jihar Nasarawa.

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wata malamar makarantar firamare, Amina Hussaini, a gidanta da ke ƙauyen Kuru, Ƙaramar Hukumar Toto ta Jihar Nasarawa.

Wata ’yar uwarta, Suwaiba Abdullahi, ta ce an sace malamar ne ranar Talata, lokacin da mijinta yake wani aiki a Lafia.

Ta bayyana cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalinta tare da neman Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa domin sakin ta.

Suwaiba ta ce iyalin na cikin damuwa kan yadda za su tara kuɗin, inda masu garkuwar suka katse waya lokacin da aka yi ƙoƙarin roƙon su rage kuɗin.

Ta ƙara da cewa an kai rahoton lamarin ga ’yan sanda, tare da yin kira ga jami’an tsaro da gwamnatin Nasarawa da su taimaka wajen kuɓutar da malamar cikin ƙoshin lafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments