Duk da tura ƙarin motocin yaƙi da jami’an tsaro domin ƙarfafa tsaro a yankin Millennium City da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna, har yanzu mazauna yankin na cikin fargabar sace mutane.
Wasu mazauna yankin sun ce ganin motocin jami’an tsaro da sintiri lokaci-lokaci bai wadatar wajen dawo musu da kwanciyar hankali ba, domin har yanzu suna fargabar masu garkuwa da mutane.
Wani mazaunin yankin ya ce ko da yake a yanzu ba a samu wani sabon hari ba, amma har yanzu ba sa iya barci cikin kwanciyar hankali saboda barazanar sace mutane.
Wani kuma ya zargi wasu mutanen da ke zaune tare da su da taimaka wa masu garkuwa da bayanan sirri kan mazauna yankin da motsinsu. Ya bukaci gwamnati ta mayar da hankali kan gano waɗanda ke taimaka wa miyagun.
Al’ummomin Millennium City, Angwan Makama, Janruwa, Bagado, Mahuta da Mararaban Rido na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, lamarin da ke jefa iyalai cikin damuwa kan lafiyar ’ya’yansu da sauran jama’a.
Mazauna yankin sun ce abin da za su fi so shi ne ganin an dakile sace-sacen mutane tare da tarwatsa ƙungiyoyin masu garkuwa, domin su samu damar zuwa makaranta, gona da sauran harkokinsu ba tare da fargaba ba.