Za a gudanar da sallar jana’izar marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka a yau Juma’a, a fadar Sarkin Katsina, da misalin ƙarfe 2:00 na rana, bayan kammala sallar Juma’a.
An shirya gudanar da jana’izar ne domin yi wa malamin addu’a tare da rakiyarsa zuwa makwancinsa na ƙarshe. Ana sa ran ’yan uwa, almajirai, abokan arziki da sauran al’umma za su halarta.
Marigayi Sheikh Masussuka ya rasu ne sakamakon harbin bindiga da wasu mahara suka yi masa a Katsina. Rahotanni sun nuna cewa an kai masa harin ne a kusa da gidansa.
Lamarin ya jawo alhini a tsakanin al’umma, musamman almajiransa da waɗanda suka san malamin. Mutane da dama sun nuna jimamensu tare da yin addu’ar Allah ya gafarta masa.
Haka kuma, ana ci gaba da kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata kisan tare da hukunta su bisa doka.