Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiKotu ta soke takarar Atiku Abubakar, ta kuma rushe shugabancin David Mark...

Kotu ta soke takarar Atiku Abubakar, ta kuma rushe shugabancin David Mark na ADC

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke dukkan matakan da suka kai ga fitowar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke dukkan matakan da suka kai ga fitowar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027.

Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, inda ya kuma soke fitowar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, Rauf Aregbesola da wasu a matsayin shugabannin jam’iyyar na ƙasa.

Kotun ta kuma soke takarar dukkan waɗanda jam’iyyar ta tsayar domin zaɓen 2027, bisa hujjar cewa shugabancin da ya fitar da su bai halatta ba.

Mai shari’a Lifu ya amince da ƙarar Nafiu Bala Gombe, Mataimakin Shugaban Ƙasa na ADC, wanda ya yi zargin cewa David Mark da Rauf Aregbesola sun karɓi shugabancin jam’iyyar ba bisa ƙa’ida ba.

Gombe ya bayyana cewa bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ralph Nwosu, kundin tsarin mulkin ADC ya ba shi damar karɓar ragamar shugabancin jam’iyyar.

A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025, ya nemi kotu ta soke dukkan matakan da shugabancin David Mark ya ɗauka, tare da hana Mark, Aregbesola da sauran mambobin kwamitin rikon kwarya ci gaba da gabatar da kansu a matsayin halastattun shugabannin jam’iyyar.

Sai dai Sakataren Jinƙai na ADC na ƙasa, Nkemakolam Ukandu, wanda aka shigar cikin ƙarar a matsayin mai ruwa da tsaki, ya ce jam’iyyar za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments