Friday, November 6, 2026
HomeSiyasaADC ta yi watsi da hukuncin kotu kan shugabancinta, ta ce za...

ADC ta yi watsi da hukuncin kotu kan shugabancinta, ta ce za ta daukaka kara

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar (ADC) ya yi watsi da hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke kan shugabancin jam’iyyar, yana mai cewa hukuncin ya rasa tasirin da zai iya yi saboda akwai wani hukuncin kotu da aka riga aka yanke kan batun.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na kwamitin, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, ADC ta bayyana hukuncin a matsayin wanda ya riga ya tsufa ta fuskar shari’a, tare da tabbatar da cewa tawagar lauyoyinta za ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantarsa.

Kwamitin ya ce Mai Shari’a Musa Liman na wannan kotu ya riga ya yi hukunci kan batun shugabancin Sanata David Mark da Ogbeni Rauf Aregbesola, inda ya tabbatar da cewa sauyin shugabanci daga hannun Chief Ralph Nwosu zuwa hannun Mark bai saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.

Sanarwar ta bayyana cewa taron masu ruwa da tsaki na ranar 2 ga Yuli, 2025, ya kasance kafin taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (NEC) na ranar 29 ga Yuli, 2025, wanda a cikinsa aka zaɓi David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa, yayin da Rauf Aregbesola ya zama sakataren jam’iyyar.

Ta ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sa ido kan taron NEC ɗin.

ADC ta ce ba za a iya yin watsi da hukuncin da aka riga aka yanke ta hanyar wani hukunci na baya ba tare da bin ƙa’idojin shari’a ba. Saboda haka, ta bayyana cewa za ta nemi matakin shari’a da ya dace, ciki har da neman dakatar da aiwatar da sabon hukuncin idan doka ta ba da dama.

Kwamitin ya kuma nuna damuwa kan lokacin da aka yanke hukuncin, inda ya danganta hakan da nasarar ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ADC a Sakkwato, da kuma abin da ya bayyana a matsayin gazawar APC wajen ƙaddamar da nata yaƙin neman zaɓe a Kaduna.

Ya yi zargin cewa jam’iyyar APC na ƙoƙarin amfani da wasu hanyoyi wajen kawo cikas ga ci gaban ADC.

Haka kuma, ADC ta yi zargin cewa akwai matsin lamba da katsalandan na siyasa a cikin shari’ar, tana mai kira da a kare ’yancin kai da martabar bangaren shari’a.

Ta kuma tuna cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta taɓa soke wani hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke a baya kan soke rajistar jam’iyyar.

A ƙarshe, kwamitin ya tabbatar da cewa David Mark na nan a matsayin shugaban jam’iyyar, yayin da Rauf Aregbesola ke ci gaba da zama sakataren jam’iyyar bisa matsayinta.

Ya kuma yi kira ga ’yan takara da magoya bayan ADC da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da yaƙin neman zaɓensu, yana mai cewa jam’iyyar za ta ci gaba da ƙalubalantar hukuncin ta hanyar kotu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments