Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi barazanar korar duk wani jami’in siyasa ko ɗan jam’iyya da aka kama yana sayar da kayan tallafin ƙarfafa tattalin arziki da aka raba wa al’umma.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, a wajen bikin ƙarfafa tattalin arzikin al’umma karo na 12 da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu, ya gudanar ranar Litinin.
Gwamnan ya jaddada cewa ba za a lamunci sayar da kayan tallafin da aka raba domin amfanin al’umma ba, tare da yin barazanar ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu da laifin karkatar da su domin wata manufa ta daban.