Friday, November 6, 2026
HomeLabarai’Yan Najeriya za su tuna da tsadar rayuwa fiye da addu’ar Tinubu...

’Yan Najeriya za su tuna da tsadar rayuwa fiye da addu’ar Tinubu a Makka – Phrank Shuaibu

Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Phrank Shaibu, ya soki tafiyar Shugaba Bola Tinubu zuwa Saudiyya domin gudanar da Umrah, yana mai cewa ba za a tabbatar wa kowa da wa’adi na biyu ta hanyar iƙirarin samun goyon bayan Allah ba.

Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Phrank Shaibu, ya soki tafiyar Shugaba Bola Tinubu zuwa Saudiyya domin gudanar da Umrah, yana mai cewa ba za a tabbatar wa kowa da wa’adi na biyu ta hanyar iƙirarin samun goyon bayan Allah ba.

Shaibu ya ce gudanar da ibada a ƙasa mai tsarki abu ne na mutum da kansa, ba wai abin da ya kamata a mayar da shi harkar ƙasa ba. Ya zargi magoya bayan Tinubu da siyasantar da ibadar shugaban ƙasar.

Ya kuma nuna shakku kan sahihancin addinin shugaban ƙasar, inda ya ce da gaske Tinubu yana da cikakken imani, da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ba zai ci gaba da kasancewa a tsare ba.

Shaibu ya ƙara da cewa ikirarin gwamnatin Tinubu na cewa tattalin arzikin ƙasar ya inganta ba gaskiya ba ne, duba da yadda ’yan Najeriya da dama ke fama da tsadar rayuwa.

Ya ce ’yan Najeriya za su tuna da addu’ar Tinubu a Makka kamar yadda suke tuna tsadar abinci da sauran kayayyaki da ayyuka.

Da aka tambaye shi ko tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai raka Tinubu Saudiyya idan aka gayyace shi, Shaibu ya ce Atiku ne ya ɗauki nauyin tafiyar farko ta Tinubu zuwa Makka.

Dangane da damar Atiku a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, musamman a jihohin Arewa, mai magana da yawun ya ce Atiku yana da ƙwarin gwiwar samun nasara a yankin.

Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa Makka a ranar 29 ga Oktoba domin gudanar da ibadar Umrah, inda ya ce ya roƙi Allah Ya ba Najeriya da al’ummarta jagoranci nagari da albarka.

Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa Allah ne ke ba da mulki, kuma yana da imanin cewa an ba shi damar jagorantar Najeriya domin ya yi amfani da ita yadda ya kamata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments