Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiNCDC: Barkewar Ebola na iya janyo dage zaɓen 2027 a Najeriya

NCDC: Barkewar Ebola na iya janyo dage zaɓen 2027 a Najeriya

Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa (NCDC) ta ce za a iya duba yiwuwar dage babban zaɓen 2027 idan barkewar cutar Ebola ta bazu sosai a Najeriya har ta zama barazana ga gudanar da zaɓen.

Darakta-Janar na hukumar, Dr. Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026.

Sai dai Idris ya jaddada cewa a halin yanzu babu buƙatar dage zaɓen, yana mai fatan cewa za a shawo kan barkewar cutar kafin ta kai matakin da zai kawo cikas ga tsarin zaɓen.

Ya bayyana cewa hukumar ta daɗe tana sanya ido kan barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), inda ta yi la’akari da yiwuwar cutar ta shigo Najeriya sakamakon zirga-zirgar jama’a tsakanin ƙasashe da kuma zirga-zirgar jiragen sama.

Haka kuma, shugaban NCDC ya yi gargaɗin cewa bai kamata a yi amfani da matsalolin lafiya a matsayin makamin siyasa ba, yana mai cewa ya kamata a mayar da hankali wajen kare lafiyar al’umma da shawo kan cutar.

Duk da wannan bayani, babu sanarwar hukuma da ta nuna an dage zaɓen 2027.

Yiwuwar dagewar za ta dogara ne da yadda yanayin barkewar cutar zai kasance da matakan da hukumomin da abin ya shafa za su ɗauka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments