Majalisar tarayya ta aika wa Shugaba Bola Tinubu kudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai ba da damar kafa rundunonin ’yan sandan jihohi domin ya sanya hannu a kai.
Wannan mataki ya biyo bayan amincewar majalisun dokokin jihohi 29 daga cikin 36, lamarin da ya wuce adadin kashi biyu bisa uku da kundin tsarin mulki ya tanada.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar a ranar Laraba, bayan karanta sanarwar magatakardar majalisar tarayya, Kamoru Ogunlana.
Sanarwar ta ce an samu sahalewar majalisun jihohin ne zuwa ƙarshen ranar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026, don haka aka umurci magatakardar ya aika da kudirin ga shugaban ƙasa a ranar Laraba.
Idan Tinubu ya sanya hannu, jihohi za su samu damar kafa tare da gudanar da rundunonin ’yan sandansu, matakin da ake sa ran zai taimaka wajen tattara bayanan sirri da inganta tsaro a faɗin ƙasar.