Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta amince da biyan Naira 100,000 duk mako ga mutanen da aka killace ko sanya ido a kansu saboda Ebola a Abuja.
Darektan hukumar, Dakta Jide Idris, ya ce an ɗauki matakin ne domin taimaka musu wajen biyan kuɗin abinci, masauki da kula da iyalansu yayin da suke bin ƙa’idojin killacewa.
Ya bayyana cewa tallafin bai cikin shirin farko ba, amma ya zama dole saboda ƙalubalen da waɗanda ake sa ido a kansu ke fuskanta. Ya kuma jaddada cewa sauran jihohi na buƙatar tanadin kuɗi da kayan aiki domin tunkarar irin wannan annoba.
A lokacin da aka yi bayanin, NCDC ta ce an tabbatar da mutum ɗaya ya kamu da Ebola a Najeriya, yayin da aka gano mutane 53 da suka yi hulɗa da shi.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da sa ido kan waɗannan mutane har tsawon kwanaki 21 bayan yiwuwar kamuwarsu da cutar, tare da yi musu gwaje-gwaje idan sun nuna alamun Ebola.