Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiAtiku ya buƙaci INEC ta bayyana jami’an da suka shigar da hotunan...

Atiku ya buƙaci INEC ta bayyana jami’an da suka shigar da hotunan AI cikin rajistar masu zaɓe

Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci INEC ta bayyana sunayen jami’an da ake zargi da shigar da hotunan da aka samar ta hanyar fasahar AI cikin rajistar masu zaɓe.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci INEC ta bayyana sunayen jami’an da ake zargi da shigar da hotunan da aka samar ta hanyar fasahar AI cikin rajistar masu zaɓe.

A cikin sanarwar da daraktan yaɗa labaran yaƙin neman zaɓensa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce lamarin abin kunya ne da ke barazana ga amincewar jama’a ga hukumar.

Ya buƙaci ’yan adawa da ƙasashen duniya su nemi gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano gaskiyar lamarin, tare da bayyana hujjoji da kuma hukunta waɗanda aka samu da laifi.

Atiku ya kuma zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da barin INEC ta kauce wa bincike, yana mai cewa bai kamata hukumar ta nemi amincewar jama’a alhali tana ɓoye bayanai kan waɗanda ake zargi ba.

Ya kuma buƙaci gudanar da cikakken binciken fasaha kan rajistar masu zaɓe, musamman bisa zargin cewa hotunan AI na iya kai wa sama da miliyan 20. Ya gargaɗi cewa rashin magance matsalar na iya shafar amincewar jama’a ga zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments