Saturday, November 7, 2026
HomeSiyasa2027: Kwankwaso ya samu sabon muƙami a kwamitin yaƙin neman zaɓen NDC

2027: Kwankwaso ya samu sabon muƙami a kwamitin yaƙin neman zaɓen NDC

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar Najeriya na jam’iyyar NDC, ya samu muƙamin mataimakin shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar na ƙasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Sanarwar da jam’iyyar ta fitar ta nuna cewa an naɗa Kwankwaso a matsayin mataimakin shugaban kwamitin, yayin da Sanata Henry Seriake Dickson, jagoran jam’iyyar na ƙasa, zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba.

Haka kuma, Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, zai kasance mataimakin shugaban kwamitin, yayin da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Cleopas Moses Zuwoghe, zai zama mataimakin shugaban kwamitin na farko.

Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Barrista Ikenna Morgan Enekweizu, sakataren jam’iyyar na ƙasa, wanda zai zama sakataren kwamitin, da Mallam Ibrahim Hussain Abdulkarim, wanda zai jagoranci ayyukan kwamitin a matsayin Darakta Janar.

A cewar sanarwar, kwamitin zai jagoranci tsara dabarun yaƙin neman zaɓe, daidaita ayyukan kamfen a faɗin Najeriya da kuma tattara goyon bayan jama’a ga manufofin jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027, wanda ake sa ran zai kasance gasa mai zafi tsakanin manyan ’yan takara da jam’iyyun siyasar ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments