Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba ɗaya ta fara sauraron shaidu a shari’ar Maimuna Idris, wadda ake zargi da yanke gaban saurayinta, Ashiru Sani.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an fara sauraron shari’ar ne a harabar kotuna ta Audu Bako da ke Kano.
A zaman kotun na ranar Lahadi, lauyan masu gabatar da ƙara, Barrister Safiya Yalwati Yahaya, ta gabatar da Ashiru Sani a matsayin babban shaida domin ya bayyana abin da ya faru tsakaninsa da wadda ake tuhuma.
A cikin bayanin da ya yi a gaban kotun, Sani ya yi zargin cewa Maimuna ta ba shi wani magani mai suna Diazepam, wanda ya ce ya sa ya rasa hayyacinsa kafin faruwar lamarin da ake tuhumarta a kai.
Bayan kammala bayanin nasa, kotun ta sallame shi daga bayar da shaida a wannan zama, sannan ta ɗage shari’ar zuwa ranar 19 ga Nuwamba, 2026, domin ci gaba da sauraron shaidu.
Rahoton ya ce ana zargin Maimuna da aikata laifin ne a wani ɗakin shakatawa.
Sai dai, a wani zaman kotu da ya gabata, ta musanta zargin da ake yi mata.
Ana sa ran kotun za ta ci gaba da sauraron shaidun masu gabatar da ƙara a zaman da aka sanya, kafin ta tantance hujjojin da aka gabatar tare da yanke hukunci bisa tanadin doka.