Friday, November 6, 2026
HomeSiyasaGoyon bayan Tinubu a Arewa na nan daram – Musa Illiyasu Kwankwaso

Goyon bayan Tinubu a Arewa na nan daram – Musa Illiyasu Kwankwaso

Jigo a jam’iyyar APC kuma mamba a Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar (PCC), Dr. Musa Illiyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa magoya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a yankin Arewa sun ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan sake zaɓensa a shekarar 2027.

Kwankwaso ya ce babu fargaba ko ja da baya a tsakanin magoya bayan shugaban ƙasar kan batun sake zaɓensa a wa’adin mulki na gaba.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a lokacin wata ziyarar aiki ta jam’iyyar APC zuwa Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.

A cewarsa, Shugaba Tinubu shi ne mutumin da ya dace ya ci gaba da jagorantar Najeriya bayan zaɓen 2027, yana mai jaddada cewa goyon bayan da shugaban ƙasar ke samu daga Arewa yana nan daram kuma ba zai girgiza ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments