Tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriya, Yakubu Dogara, ya ce matsalar rashin tsaro a ƙasar ba ta fara ne a zamanin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba, domin ta daɗe tana addabar Najeriya tun kafin shekarar 2023.
Dogara ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye ɗalibai karo na 16 na jami’ar Achievers da ke Owo, jihar Ondo, inda aka yaye ɗalibai 836 tare da ba su takardun shaidar kammala karatu daban-daban.
Ya ce ta’addanci, ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da rikice-rikicen al’umma sun samo asali ne daga matsalolin da suka daɗe, ciki har da raunin tsaron iyakoki, yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba, rashin aikin yi da yaɗuwar akidun tsattsauran ra’ayi.
Sai dai Dogara ya jaddada cewa hakan ba yana nufin gwamnatin Tinubu ba ta da alhakin magance matsalar ba, yana mai cewa Shugaban ƙasar ya sha bayyana tsaro a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.
A nasa jawabin, shugaban jami’ar, Farfesa Omolola Irinoye, ya ce jami’ar na ci gaba da samar da ingantaccen ilimi da ke haɗa ƙwarewar aiki, tarbiyya da ci gaban tunani, yayin da shugaban jami’ar, Farfesa Bode Ayorinde, ya nuna damuwa kan irin damar aikin yi da ke jiran ɗalibai bayan kammala karatu.