Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Peter Obi, Atiku Abubakar da sauran manyan shugabannin siyasa bisa taya shi murnar cika shekara 70 da haihuwa.
Nasara Radio ta rawaito cewa Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin saƙon godiya da ya fitar ranar Lahadi, inda ya nuna jin daɗinsa bisa addu’o’i da saƙonnin fatan alheri da ya samu daga shugabannin siyasa, iyalansa, abokai da magoya bayansa.
Tsohon gwamnan Kano ya kuma miƙa godiyarsa ga tsoffin shugabannin Najeriya, Olusegun Obasanjo, Ibrahim Babangida, Abdulsalami Abubakar da Goodluck Jonathan, bisa taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Haka kuma, Kwankwaso ya gode wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, tare da sauran shugabannin da suka halarci bikin.
Ya kuma yaba wa shugabannin jam’iyyar NDC, ’yan jarida, jami’an tsaro da magoya bayansa bisa gudummawar da suka bayar wajen gudanar da bikin.
A ƙarshe, Kwankwaso ya roƙi Allah Ya saka wa kowa da alheri, Ya albarkaci Najeriya, tare da ba al’ummar ƙasar ƙarfi da hikimar samar da ci gaba, haɗin kai da wadata.