Friday, November 6, 2026
HomeTsaroJami’an tsaro sun ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su...

Jami’an tsaro sun ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Jami’an tsaro sun yi nasarar ceto mutane takwas da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna, ciki har da wata mata mai suna Jamila Muhammad, mai shekaru 27, wadda rahotanni suka ce ta rasa cikin da take ɗauke da shi a lokacin da take hannun masu garkuwar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gudanar da aikin ceton ne tsakanin ranar 31 ga Oktoba zuwa 2 ga Nuwamba, ta hanyar haɗin gwiwar Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA), Hukumar DSS, rundunar ’yan sanda da sojoji, tare da gwamnatin Jihar Kaduna.

An yi garkuwa da Jamila ne a ranar 6 ga Oktoba, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai hari a unguwar Alrahus Estate da ke Millennium City, Ƙaramar Hukumar Chikun.

A yayin harin, maharan sun sace ta tare da Ahmad Zakka, matarsa da jaririyarsu mai watanni shida. Daga baya, Zakka da iyalansa sun samu ’yanci a ranar 15 ga Oktoba, bayan da wani bidiyonsu da ke hannun masu garkuwar ya yaɗu a kafafen sada zumunta. Sai dai Jamila ta ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwar har zuwa lokacin da aka ceto ta.

Sauran mutanen da aka ceto sun haɗa da Talatu Yakubu, mai shekaru 40; Yunana Bawa, mai shekaru 30; Calista Bishop, mai shekaru 27; Chidinma Onuwere, mai shekaru 36; Eucharia Obi, mai shekaru 41; Godiya Victor, mai shekaru 50; da Miracle Alex, yarinya mai shekaru takwas.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Muhammad Rabiu, ne ya bayyana nasarar ceton mutanen yayin wani taron manema labarai a hedikwatar DSS da ke Kaduna.

Ya ce aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin jami’an tsaro na gano tare da tarwatsa ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane a Millennium City da yankunan da ke kewaye.

Kwamishinan ya yaba da haɗin kan ONSA, DSS, ’yan sanda, sojoji da gwamnatin Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani wajen samun nasarar aikin.

Ya kuma bayyana cewa za a ƙara tura jami’an tsaro da kayan aiki zuwa yankin, ciki har da motocin sintiri guda 30 da motocin yaƙi masu sulke guda takwas, domin inganta tsaro.

A ƙarshe, ya buƙaci al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani motsi ko mutum da suke zargi ga jami’an tsaro, yana mai tabbatar da cewa za a kiyaye sirrin waɗanda suka bayar da bayanan sirri.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments