Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiACF ta nada jagoran riko a Kano bayan shugaban kungiyar ya yi...

ACF ta nada jagoran riko a Kano bayan shugaban kungiyar ya yi murabus

Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) reshen Jihar Kano ta naɗa mutum uku a matsayin shugabancin riƙo bayan murabus ɗin shugabanta, Dr Goni Faruk Umar.

Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) reshen Jihar Kano ta naɗa mutum uku a matsayin shugabancin riƙo bayan murabus ɗin shugabanta, Dr Goni Faruk Umar.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar a Kano, Nasiru Yusuf Ibrahim, ya ce matakin na cikin ƙoƙarin dawo da haɗin kai da warware saɓanin cikin gida da ya shafi ayyukan ƙungiyar.

Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Dagacin Tofa, Alhaji Isyaku Umar Tofa; Ambasada Bala Mohammed Sani da Hajiya Rabia Husaini Adamu. Janar mai ritaya, Haliru Akilu, ne ya sanar da naɗin yayin wani taron shugabannin ƙungiyar a Kano ranar Asabar.

Akilu ya ce shugabancin riƙon zai jagoranci ƙungiyar har zuwa ƙarshen wa’adin shugabancin yanzu, ko kuma a zaɓi sabon shugaba. Ya buƙaci mambobin su ajiye saɓaninsu gefe guda, su fifita sulhu da haɗin kai domin inganta ayyukan ƙungiyar.

Ya tabbatar da karɓar takardar murabus ɗin Dr Umar, wanda ya ce yawan ayyukansa ne ya sa ya ajiye mukamin. Ya kuma yaba wa Alhaji Abubakar Idris Ahmed, wanda ya riƙe shugabancin na kusan watanni huɗu, yayin da sababbin shugabannin riƙon suka yi alƙawarin dawo da haɗin kai da ingantaccen gudanarwa har sai an zaɓi sabon shugaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments