Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabarai’Yan sandan Jihar Ogun sun kama Saburi Lateef, mai shekaru 49, bisa...

’Yan sandan Jihar Ogun sun kama Saburi Lateef, mai shekaru 49, bisa zargin kashe tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati, Adedotun Oluwaseun, a gidanta da ke Abeokuta

Rahotanni sun ce Lateef, wanda aka fi sani da Alhaji Oki Osan, ya amsa cewa ya shake matar sannan ya yi mata raunuka da adduna. An kama shi ne bayan sama da watanni 10 da kisan.

Ana zargin ya shiga gidanta ne domin satar kuɗin ritayarta, amma ya gamu da ita bayan ta dawo gida. Sai dai shi ya ce rikicin kuɗi naira miliyan 3.45 da ya ba ta ne ya jawo sabani tsakaninsu.

Babbar ’yar marigayiyar, Taiwo Atanda, ta musanta cewa iyalansu sun san wanda ake zargin ko wata mu’amalar kuɗi tsakaninsa da mahaifiyarsu. Ta ce sun gan shi a karon farko ne bayan kisan, lokacin da ya zo gidan cikin masu ta’aziyya.

Iyalan marigayiyar sun roƙi ’yan sanda da gwamnatin jihar su tabbatar an yi adalci. Kakakin ’yan sandan Ogun, DSP Oluseyi Babaseyi, ya tabbatar da kama wanda ake zargin, yana mai cewa za a ci gaba da bincike domin gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.

’Yan sandan Jihar Ogun sun kama Saburi Lateef, mai shekaru 49, bisa zargin kashe tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati, Adedotun Oluwaseun, a gidanta da ke Abeokuta.

Rahotanni sun ce Lateef, wanda aka fi sani da Alhaji Oki Osan, ya amsa cewa ya shake matar sannan ya yi mata raunuka da adduna. An kama shi ne bayan sama da watanni 10 da kisan.

Ana zargin ya shiga gidanta ne domin satar kuɗin ritayarta, amma ya gamu da ita bayan ta dawo gida. Sai dai shi ya ce rikicin kuɗi naira miliyan 3.45 da ya ba ta ne ya jawo sabani tsakaninsu.

Babbar ’yar marigayiyar, Taiwo Atanda, ta musanta cewa iyalansu sun san wanda ake zargin ko wata mu’amalar kuɗi tsakaninsa da mahaifiyarsu. Ta ce sun gan shi a karon farko ne bayan kisan, lokacin da ya zo gidan cikin masu ta’aziyya.

Iyalan marigayiyar sun roƙi ’yan sanda da gwamnatin jihar su tabbatar an yi adalci. Kakakin ’yan sandan Ogun, DSP Oluseyi Babaseyi, ya tabbatar da kama wanda ake zargin, yana mai cewa za a ci gaba da bincike domin gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments