Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya ce duk ɗan Arewa da ke neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2027 maƙiyin yankin ne, yana mai cewa lokacin Arewa na komawa kan mulki shi ne 2031.
Akume ya bayyana hakan ne ranar Asabar a wani taro da ’yan asalin Benue da ke zaune a Kaduna, a ranar da APC ta ƙaddamar da kamfen ɗin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.
Ya ce an cimma yarjejeniyar karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu a Kaduna domin kiyaye haɗin kan Najeriya. Saboda haka, ya buƙaci ’yan Arewa su goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027.
Akume ya gargaɗi ’yan Arewa da kada su bari burin siyasar wasu mutane ya raba kan yankin ko ya raunana tasirinsa. Ya kuma ce bai kamata a bari siyasa ta haddasa rarrabuwar kai bisa addini ko muradun kansu ba.
Da yake kare Tinubu, Akume ya ce shugaban na yin adalci wajen naɗe-naɗen mukamai, tare da gudanar da ayyukan raya ƙasa a Benue da sauran jihohi. Ya kuma soki Atiku Abubakar kan matsayinsa game da cire tallafin man fetur.