Wasu ’yan bindiga sun kashe mambobin rundunar sa-kai bakwai tare da sace mutane da dama a garin Kaura Namoda da ke Jihar Zamfara, bayan sun shafe sama da sa’o’i uku suna kai hari a garin.
Shugaban ƙaramar hukumar Kaura Namoda, Munnir Haidara, ya tabbatar da mutuwar ’yan rundunar haɗin gwiwa ta JTF bakwai. Ya ce harin ya shafi yankunan Kofar Zurmi da tsohuwar kasuwa, yayin da wasu ’yan sa-kan suka jikkata.
Haidara ya ce har yanzu suna tattara bayanai domin tantance adadin mutanen da aka sace. Sai dai wani mazaunin garin ya shaida wa Daily Trust cewa waɗanda aka sace na iya haura 30, ciki har da wasu ’ya’yan wani malamin addinin Musulunci.
Wani mazaunin garin ya ce maharan sun bi wata hanya ta gefen kogi wajen shiga garin, inda suka kauce wa wuraren da ’yan sa-kai suka saba gadin. Ya kuma yi zargin cewa ƙarancin makaman ’yan sa-kan ya taimaka wajen bai wa ’yan bindigar damar kai harin.
Sai dai Haidara ya musanta zargin cewa an kai jami’an tsaro Kaduna domin halartar gangamin kamfen ɗin Tinubu, yana mai cewa waɗanda suka tafi magoya bayan siyasa ne kawai. Ya ce shi ne ya tsara tafiyar mutanen da suka je Kaduna cikin motoci 10, kuma babu wani jami’in tsaro da aka tafi da shi.