Monday, October 19, 2026
HomeKasashen wajeAn harbi motar jarumi Tiger Shroff a Mumbai, direbansa da wani sun...

An harbi motar jarumi Tiger Shroff a Mumbai, direbansa da wani sun ji rauni

Wasu mahara da ba a tantance ko su waye ba sun buɗe wuta kan motar jarumin fina-finan Indiya, Tiger Shroff, a yankin Juhu da ke birnin Mumbai.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi, lokacin da jarumin ke barin filin ƙwallon ƙafa a cikin motarsa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna wasu mutane suna harbin motar daga kusa yayin da take tafiya a hankali a cikin taron jama’a.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa Tiger Shroff bai samu raunin harbin bindiga ba, yayin da direbansa da wani mutum suka samu raunuka a harin, lamarin da ya sa aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.

Bayan faruwar lamarin, ’yan sanda sun kafa tawagogi da dama domin gudanar da bincike, tattara shaidu da kuma nazarin hotunan kyamarorin tsaro da nufin gano waɗanda suka kai harin.

Ya zuwa yanzu, ba a bayyana sunayen waɗanda ake zargi da kai harin ko dalilin aikata shi ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments