Monday, October 19, 2026
HomeSiyasaZamfara: ’Yan majalisa takwas na shirin komawa APC bayan ganawa da Tinubu

Zamfara: ’Yan majalisa takwas na shirin komawa APC bayan ganawa da Tinubu

’Yan majalisar dokokin Jihar Zamfara guda takwas da suka fice daga jam’iyyar APC mai mulki sun bayyana aniyarsu ta komawa jam’iyyar bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ne ya jagoranci ’yan majalisar zuwa ganawar da shugaban ƙasar, kamar yadda Ahmad Dan-Wudil, mai taimaka wa tsohon gwamnan Zamfara kan harkokin yaɗa labarai, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Sanarwar ta ce yayin ganawar, ’yan majalisar sun sake jaddada amincinsu da goyon bayansu ga APC da Shugaba Tinubu.

Ta ƙara da cewa Matawalle ya yi alƙawarin shigar da su cikin ƙungiyar Tinubu Again Movement domin su haɗa kai wajen yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da sauran ’yan takarar APC a zaɓuka masu zuwa.

’Yan majalisar sun fice daga APC a farkon watan Oktoba, inda suka bayyana tabarbarewar tsaro, rashin adalci da kuma rashin biyan albashi da alawus-alawus a matsayin dalilan matakin da suka ɗauka.

’Yan majalisar sun haɗa da Aliyu Kagara mai wakiltar Talata Mafara ta Kudu; Ibrahim Bakura na Bakura; Faruk Dosara na Maradun I; Bashir Masama na Bukkuyum ta Arewa; Muktaru Kaura na Kaura ta Arewa; Nasiru Abdullahi na Maru ta Arewa; Bashar Bello na Bungudu ta Yamma; da Bashar Aliyu na Gummi I.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments