Monday, October 19, 2026
HomeSiyasaGwamnan Kano Abba zai jagoranci Arewa wajen ƙara wa Tinubu ƙuri’u a...

Gwamnan Kano Abba zai jagoranci Arewa wajen ƙara wa Tinubu ƙuri’u a 2027

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa yankin Arewa zai goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙoƙarinsa na sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A) a Abuja, kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa a ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026.

Abba ya ce ƙaddamar da ofishin ya nuna aniyar al’ummar Arewa na tallafa wa Tinubu, yana mai cewa ƙungiyar za ta taimaka wajen tattara goyon baya ga shugaban ƙasar a faɗin jihohin yankin gabanin zaɓen 2027.

Gwamnan ya kuma bayyana Kano a matsayin muhimmiyar jiha wajen samar da ƙuri’u, yana mai cewa za ta jagoranci sauran jihohin Arewa wajen ƙarfafa fitowar masu kaɗa ƙuri’a domin tallafa wa Tinubu.

Ƙungiyar A4A, wadda tsohon Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ke jagoranta, ta bayyana manufarta a matsayin tallata ayyukan gwamnatin Tinubu da kuma tattara goyon baya ga tikitin Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, a zaɓen 2027.

Tinubu na shirin neman wa’adi na biyu a matsayin shugaban ƙasar a zaɓen da za a gudanar a shekarar 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments