Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsu ba za ta janye takararta ta shugaban ƙasa domin marawa ADC ko wata jam’iyya baya a zaɓen 2027 ba, yana mai zargin kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC da ƙoƙarin ɓatawa jam’iyyarsu suna.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata sanarwa, inda ya ce ya nuna damuwa kan hare-haren da ake kai masa, ɗan takarar shugaban ƙasar NDC, Peter Obi, da kuma jam’iyyar.
Ya zargi kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC da ƙoƙarin yaɗa zargin cewa NDC na yi wa APC aiki, ko kuma za ta janye takararta a minti na ƙarshe domin marawa ɗan takarar ADC baya.
Ya ce maimakon ADC ta mayar da hankali kan sukar NDC, ya kamata ta yi bayani kan zarge-zargen da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi wa ɗan takararta.
Kwankwaso ya jaddada cewa tikitin takarar Peter Obi da abokin takararsa, wanda ya kira OK ticket, ba ya aiki a madadin APC ko wani ɗan takararta, kuma ba su da niyyar janyewa wata jam’iyya.
Ya kuma soki gwamnatin APC, yana mai cewa ta gaza wajen biyan buƙatun ’yan Najeriya, sannan ya ce ADC ba ta bayar da wata mafita mafi kyau ba. A cewarsa, tikitin NDC yana da ƙwarewa, sahihanci da goyon baya daga Arewa da Kudu.
Ya bayyana cewa tikitin nasu zai mayar da hankali kan haɗa kan ’yan Najeriya da magance matsalolin tsaro, ilimi, noma, ababen more rayuwa, kiwon lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe, Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayan NDC da sauran ’yan Najeriya da su ci gaba da mara wa jam’iyyar baya, yana mai jaddada cewa suna da kwarin gwiwar samun nasara a zaɓen mai zuwa.