Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi gargaɗin cewa shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje, ciki har da shinkafa daga Thailand, ya jefa kamfanonin shinkafa na cikin gida cikin matsin tattalin arziki.
Sarkin ya bayyana cewa matakin gwamnatin Najeriya na buɗe kasuwarta ga kayan abinci daga ƙetare ya raunana kamfanonin sarrafa shinkafa, tare da jefa bankunan da suka ba su rance cikin matsalar karɓar basussukansu.
Ya ce wasu kamfanonin sun gaza biyan bashin da suka karɓa daga bankuna, duk da cewa bankunan sun zuba kuɗaɗe masu yawa a harkokin noma da nufin bunƙasa samar da abinci a cikin gida.
Muhammadu Sanusi II ya bayyana hakan ne a ƙarshen makon da ya gabata yayin wani taro kan ci gaba mai ɗorewa da aka gudanar a Legas, da ke kudancin Najeriya.
Sarkin ya jaddada muhimmancin da ke tattare da dogaro da kayan da ake nomawa da sarrafawa a Najeriya, maimakon ci gaba da dogaro da shigo da su daga ƙasashen waje.
Ya kuma yi kira da a samar da manufofin da za su tallafa wa manoma da kamfanonin cikin gida, domin ƙarfafa samar da abinci da bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.