Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiTun da Buhari ya kasa magance matsalar tsaro, bai kamata a ɗora...

Tun da Buhari ya kasa magance matsalar tsaro, bai kamata a ɗora wa Tinubu nauyi ba – Yari

Daraktan yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce bai kamata a yi tsammanin Tinubu zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya gaba ɗaya ba, bayan gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta kasa yin hakan duk da ƙwarewarsa ta soja.

Yari ya bayyana hakan ne a Jihar Kebbi yayin ganawa da gwamnan jihar da kuma sarakunan gargajiya, inda ya yi tsokaci kan matsalar tsaron da ke addabar ƙasar.

A cewarsa, Buhari, wanda ya yi ritaya daga aikin soja da muƙamin janar, ya yi ƙoƙarin shawo kan matsalolin tsaro a lokacin mulkinsa, amma bai samu nasarar kawo ƙarshensu gaba ɗaya ba.

Sai dai Yari ya jaddada cewa gwamnatin Shugaba Tinubu tana ƙoƙarin magance matsalolin tsaron da ke addabar Najeriya.

Ya bayyana cewa ya kamata a yi la’akari da irin ƙalubalen da ke tattare da matsalar tsaro, maimakon ɗauka cewa gwamnati za ta iya kawar da ita gaba ɗaya cikin sauƙi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments