Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiLabaraiNijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa kasashen waje

Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa kasashen waje

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta haramta fitar da man fetur da iskar gas daga ƙasar zuwa ƙasashen waje, a wani mataki na tabbatar da wadatar makamashi ga al’ummar ƙasar kafin sayar wa sauran ƙasashe.

Kamfanin dillancin labaran Nijar, ANP, ya ruwaito cewa Ministan Ciniki da Masana’antu na ƙasar, Abdoulaye Seydou, ne ya rattaba hannu kan dokar da ta tanadi wannan haramcin.

Dokar ta tanadi cewa idan aka samu rarar man fetur ko iskar gas bayan an biya buƙatun cikin gida, matatar man ƙasar ta SORAZ da kamfanin man Nijar na SONIDEP za su iya fitar da rarar zuwa ƙasashen waje ne kawai idan sun samu izini na musamman daga ministan da ke kula da harkokin ciniki.

Haka kuma, dokar ta umurci ma’aikatan Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu, jami’an kwastam da jami’an tsaro da su tabbatar da an bi ƙa’idojin da aka gindaya.

Matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin man fetur a gidajen mai na Yamai, babban birnin ƙasar, da wasu biranen Nijar, kamar yadda ANP ta ruwaito.

Duk da cewa Nijar ƙasa ce mai arzikin man fetur, kuma matatar SORAZ tana tace ɗanyen mai a cikin ƙasar, yawan man da ake tacewa a halin yanzu bai wadatar da buƙatun cikin gida ba.

A watan Agustan 2026, Nijar ta kuma sanya hannu kan yarjejeniyar gina sabuwar matatar mai da za ta iya tace ganga 100,000 na ɗanyen mai a kowace rana tare da wani kamfanin ƙetare, domin ƙara ƙarfin tace man fetur a ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments