Akalla mutane 1,200 ne aka kama a Faransa bayan zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa da matsalolin makarantu ta rikide zuwa tashin hankali, inda aka samu arangama da jami’an tsaro, satar kayayyaki da kona gine-gine a sassan ƙasar.
Gwamnatin Faransa ta ce kusan mutane 550,000 ne suka fito zanga-zangar a ranar Asabar. A birnin Paris, jami’an ’yan sandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da motocin watsa ruwa domin tarwatsa masu zanga-zangar, yayin da aka kona motoci da gine-gine tare da lalata shaguna.
A birnin Limoges, gobarar da ta tashi a ginin majalisar birnin ta yi sanadin ruftawar wani ɓangare na rufinsa, yayin da aka kuma ƙona ofishin yawon buɗe ido a birnin Lyon. Rahotanni sun ce an wawashe shagunan tufafi da abinci a Paris, sannan wasu sun fasa wani shagon kamfanin Apple a Lille tare da kwashe kayayyakinsa.
Firaministan Faransa, Sébastien Lecornu, ya ce jami’an ’yan sanda 150 sun jikkata a yayin rikicin. Haka kuma, magajin garin Saint-Étienne, Régis Juanico, ya bayyana cewa wani matashi ya rasa hannunsa sakamakon fashewar wani ƙaramin abu mai fashewa.
Zanga-zangar ta samo asali ne daga ƙorafe-ƙorafen ɗalibai kan ƙarancin ma’aikata da lalacewar kayayyakin more rayuwa a makarantun sakandare, tare da ƙungiyoyin ƙwadago da masu adawa da tsadar rayuwa da suka shiga cikinta.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yi alƙawarin gurfanar da hukunta duk waɗanda aka samu da hannu wajen kai hare-hare, lalata kadarori da satar kayayyaki. Yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa na ƙara kusantowa, lamarin da ya sa rikicin ya ƙara zama wani babban ƙalubale na siyasa ga ƙasar.