Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeTrump ya zargi shige da fice da haddasa rikici a Faransa, ya...

Trump ya zargi shige da fice da haddasa rikici a Faransa, ya bukaci rufe iyakoki

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya danganta tashin hankalin da ya barke a Faransa da shige da fice, inda ya bukaci gwamnatin ƙasar ta rufe iyakokinta tare da dawo da cikakken iko kan harkokin tsaro.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya danganta tashin hankalin da ya barke a Faransa da shige da fice, inda ya bukaci gwamnatin ƙasar ta rufe iyakokinta tare da dawo da cikakken iko kan harkokin tsaro.

Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Lahadi, 18 ga Oktoba, 2026, inda ya ce Faransa na cikin tashin hankali, yana mai zargin cewa shige da ficen mutanen da ya kira masu bambancin al’adu da ƙiyayya ya lalata ƙasar.

Ya ce ya kamata hukumomin Faransa su gaggauta rufe iyakokin ƙasar tare da ɗaukar matakan dawo da iko, yana mai gargaɗin cewa idan ba a yi hakan ba, lokaci zai kure.

Wannan furuci na Trump ya zo ne bayan zanga-zangar da ta barke a biranen Faransa, inda aka samu arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro, tare da kona motoci, lalata gine-gine da sace kayayyaki daga shaguna. An kuma kama mutane sama da 1,800, yayin da daruruwan jami’an tsaro da masu aikin kashe gobara suka samu raunuka.

Sai dai zanga-zangar ta samo asali ne daga koke-koken tsadar rayuwa, tabarbarewar ayyukan gwamnati da matsalolin makarantu, ciki har da ƙarancin malamai da lalacewar gine-gine. A cikin saƙonsa, Trump bai gabatar da wata hujja da ta tabbatar da cewa shige da fice ne ya haddasa tashin hankalin ba, yayin da hukumomin Faransa ke fuskantar matsin lamba na shawo kan rikicin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments